A wani labarin kuma sababbin ministocin tsaro, Muhammad Badaru Abubakar da Bello Matawalle, suna shan suka da caccaka daga ƴan Najeriya saboda rashin gogewar aiki a ɓangaren da aka ba su.
Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun ce naɗa su a matsayin manyan masu jagorantar harkar tsaro a Najeriya, na cikin abubuwa mafiya ba-zata da ban mamaki da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi.
Babban ministan tsaron, Muhammad Badaru Abubakar, ya buɗi ido ne a fagen kasuwanci da masana’antu, kafin ya faɗa siyasa. Shi ma, BelloMatawalle bai sai komai kan harkar tsaro ba, tsohon malamin makaranta ne.