A ƙoƙarinsa na tabbatar al’ummar Kano sun samu labarai game da ayyukan gwamnatinsa, gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin karin masu taimaka masa na musamman a matsayin masu ɗaukar rahoto a ma’aikatu da hukumomi daban-daban na jihar Kano.
Gwamnan, ta bakin sakataren yaɗa labaransa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana manufar wadannan naɗe-naɗe da cewa wata hanya ce ta samar da bayanai na gaskiya game da ayyuka da tsare-tsaren gwamnatin jihar Kano.
Mataimakan da sun kai 94 waɗanda suka haɗa da wasu ‘yan Jarida da ke aiki da wasu kafofin yaɗa labarai a nan Kano.
DANNA WANNAN RUBUTU DOMIN GANIN SUNAYEN MATAIMAKAN: