A ranar 28 ga watan Yunin shekarar 2022 a taron Ƙoli Na Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa da Ƙasa ne aka yanke shawarar tabbatar da wani ƙuduri na samar da tsaftataccen Yanayin Wurin Aiki a matsayin wani ɓangare na doka kuma haƙƙin ma’aikata a wuraren ayyukansu.
Wannan ta sa Ƙungiyar Ƙwadagon ta Ƙasa da Ƙasa ta keɓe a duk ranar 28 ga watan Afirilu, kamar rana ita yau, a matsayin ranar tunawa da wancan mataki da ta ɗauka kan samar da tsaftataccen muhalli a wuraren ayyuka tare da gayyato ƙwararru domin tattauna tasirin da hakan ke da shi ga sha’anin aiki a duniya da kuma hanyoyin da za a bi wajen saka wannan ƙudiri cikin jerin haƙƙoƙi na ma’aikata a wuraren ayyuka a faɗin duniya.
Sannan tun a shekarar 1996, ƙungiyar ƙwadagon ke amfani da ita wannan rana ta 28 ga watan Afrilu, wajen tunawa da Ma’aikatan da suka riga mu gidan gaskiya da kuma waɗanda suka gamu da ibtila’i a yayin ayyukansu a faɗin duniya da kuma ɗabbaƙa kiraye-kiraye domin kiyaye afkuwar ibtila’i da cutattuka a wajen ayyuka.
A kan haka muka tattauna da wani ƙwararre kuma tsohon mataimakin shugaban ƙungiyar ƙwadago reshen jihar Kano, Comr. Auwalu Mudi Yakasai, kan wannan rana.