Alhaji Abubakar Atiku, ya bukaci kotun koli ta soke hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa (PEPC) ta yanke, wanda ya tabbatar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
A cikin kunshin daukaka karar da Atiku ya shigar a gaban kotun koli, ya gabatar da hujjarsa a kan wasu dalilai 35, inda ya dage cewa kotun zabe a hukuncin da shugabanta, Mai shari’a Haruna Simon Tsammani, ya yanke, ta aikata babban kuskure da rashin adalci a sakamakon binciken da ta kammala.
Shi ma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya yi makamancin zargin tare da ɗaukaka ƙara zuwa kotun daga ke sai Allah-ya-isa.