Bayan ya shafe shekara 20 a Majalisa, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Yobe, Ahmed Mirwa Lawan, ya sha kaye a hannun matashi mai shekaru 35.
Lawan, na jam’iyyar APC dai ya sha kayen ne a hannun Lawan Musa na jam’iyyar PDP a mazabar Nguru II.
Wannan shi ne karo na biyu matashin ke fafatawa da kakakin majalisar, sai a wannan karon ne ya samu nasarar lashe zaben.
Kamar yadda jami’in tattara sakamakon zaben wannan mazaba ta Nguru Dr Habib Muhammad ya bayyana cewar,
Dan takarar Jam’iyyar ta PDP Musa Lawan ya kada kakakin majalisar Hon Ahmad Lawan Mirwa, ne da Kuri’u, da ƙuri’u dubu shida da ɗari shida da arba’in da takwas, yayin da shi kakakin majalisar dokokin ya samu Kuri’u dubu shida da ɗari huɗu da sittin da shida
Wata majiya da ke garin na Nguru ta bayyana wa majiyarmu cewa, an so a samu ‘yar hatsaniya a wannan mazaba ta Nguru sakamakon kokarin yin jinkiri shelanta wanda ya ci zaben,