Za a miƙa ƴan Najeriya da ake zargi damfara zuwa Amurka

Za a miƙa wasu ƴan Najeriya shida da hukumomin Amurka ke nema ruwa a jallo bisa zargin damfarar sama da mata 100 ta hanyar zambar soyayya a intanet daga Afirka ta Kudu zuwa Amurka a yau.

Masu gabatar da ƙara a Amurka sun ce ana tuhumar mutanen da laifin damfara da kuma halatta kuɗaɗen haram.

An yi sama da faɗi da sama da dala miliyan shida daga hannun waɗanda lamarin ya shafa, ciki har da ƴan fansho da ƴan kasuwa, waɗanda aka yi wa karyar alaƙar soyayya a intanet.

An kama waɗanda ake zargin shekara biyar da suka wuce a wani babban samame da aka kai kan wannan ƙungiyar masu aikata laifuka. Za a mika su ga jami’an tsaron Amurka a Cape Town

Post masu alaƙa

Kotun majistare ta fara sauraren shari’ar sojan gona mai mukamin CSP 

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wanda ake zargi da damfarar mutane da cewa shi babban jami’in Dan sandan ne.

Hisbah ta fara horas da sabbin jami’anta a Jigawa