Hukumar Hisbah ta Jihar Jigawa, ta fara horar da sabbin jami’anta daga Ƙananan Hukumomi 27 na jihar da kuma hedikwatar hukumar.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Dauda Muhammad Hadejia ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa.
Ya ce an fara horon a ranar Asabar, 5 ga watan Satumba, 2026, a sansanin NYSC da ke Fanisau, Dutse, kuma zai ɗauki mako guda.
A cewarsa, horon na da nufin ƙara wa jami’an ƙwarewa, inganta tarbiyya da ɗa’a, da kuma ƙara fahimtar nauyin da ke kansu wajen gudanar da ayyukan Hisbah.
Ya ce an tantance jami’an bayan sun isa sansanin, sannan aka yi musu rajista tare da ba su katin shaida da sauran kayan aikin horo.
Hadejia, ya ƙara da cewa horon zai kuma taimaka wajen ƙarfafa haɗin kai tsakanin jami’an Hisbah daga sassa daban-daban na jihar.
Hukumar ta ce inganta ƙwarewar jami’an zai taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu cikin tsari, ladabi da bin ƙa’idoji.