Home » Za A Yaƙi HIV/AIDS Gadan-Gadan A Kano

Za A Yaƙi HIV/AIDS Gadan-Gadan A Kano

by Halima Djimrao
0 comment

Ana shirye-shiryen ƙara yawan kuɗaɗen yaƙi da cutar  HIV/AIDS mai karya garkuwar jikin Ɗan Adam a jihar Kano, a wani yunƙurin rungumar hanyoyi masu ɗorewa a daidai lokacin da ake samun raguwar tallafi daga abokan hulɗa na ƙasashen waje.

Babban Darektan Hukumar yaki da cutar HIV/AIDS ta jihar Kano Dokta Usman Bashir ne ya yi wannan bayani a lokacin da ake rufe taron bita na kwanaki biyu a Kaduna wanda hukumar ta  shirya da tallafin Cibiyar Bincike da Raya Ƙasa-Ƙasa ta Solina International Development and Research.

Dokta Usman Bashir ya ce an shirya taron bitar ne don a daddale shirye-shiryen ayyukan hukumominsu su yi daidai da na ƙawayen hulɗarsu da nufin ƙarfafa ayyukan yaƙi da cutar HIV/AIDS a shekara mai zuwa ta 2024, waɗanda za su kai ga gyara yadda ake ta maimaita ayyuka iri ɗaya, don a alkinta ƴan kuɗaɗen da suka rage, kuma a kashe su inda aka fi buƙata.

Yace da ma Hukumar Yaƙi Da Cutar HIV/AIDS Ta Jihar Kano ta ɗauki matakan shirya  ma’aikatanta,  su kama ragamar aiwatar da ayyukan da ke gabansu, saboda abokan hulɗar da ke taimakawa suna ja da baya.  Kuma hukumar tana aiki wurjanjan wajen kyautata basira da dabarun aiki bisa ƙara rungumar hanyoyi masu ɗorewa.

Babban Darektan ya jinjina wa duka masu taimaka wa aikin yaki da HIV/AIDS a jihar nan wadanda suka nuna ta su basira tare kuma da karbar duka shawarwarin da masu ruwa da tsaki suka bayar.  

Dokta Usman Bashir yace jajircewar da Hukumar ta nuna irinta a karon farko, ta samar da kyakkyawan sakamako tare da tsara wani kwakkwaran shirin gudanar da ayyukan da suka dace da kudaden da gwamnati za ta kasafta.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?