Allah ya yi wa Hajiya Hajara (Uwani) rasuwa, mahaifiyar tsohon shugaban hukumar shigi da fici ta Najeriya ta Najeriya kuma mamallakin gidajen radio da talabijin na MUHASA.
Hajiya Hajara ta rasu a babban Asibitin Malam Aminu Kano da yammacin ranar Alhamis, 26 ga Disamba 2024.
Za’a yi Jana’izarta gobe Juma’a 27 ga Disamba 2024 da karfe 10 na safe a Masjid Zhera Zoo road Kano
Ta rasu bayan shafe shekaru da dama a duniya, ta bar ‘ya’ya da jikoki. Muna fatan Allah ya gafarta mata ya sa Aljanna makoma.