Hukumar zaɓe ta jihar Kano, KANSIEC, ta matso da zaɓen ƙananan hukumomi 44 da a baya ta tsara yi ranar 30 ga watan Nuwamba, 2024, zuwa ranar 26, ga watan Oktoba, 2024.
Wannan bayani na ƙunshe a jawabin da shugaban hukumar Farfesa Sani Lawan ya yi wani taron manema labarai, a yau Juma’a a hedikwatar hukumar da ke birnin dabo.
Shugaban hukumar ya ce sun yi hakan ne domin biyayya ga hukuncin Kotun Ƙoli ta Najeriya.
- Mai Shara Ya Mayar Da Dala Dubu 10 Da Ya Tsinta A Kano
- Farfesa Abdullahi (Pakistan) Ya Zama Shugaban NAHCON
Kotun ƙoli ta Najeriya dai ta bayar da wa’adin watan Oktoba domin tabbatar da cin gashin kai na ƙananan hukumomi.