Home » Za’a Iya Daƙile Cin Hanci Da Rashawa- EFCC

Za’a Iya Daƙile Cin Hanci Da Rashawa- EFCC

by Mubarak Ibrahim Mandawari
0 comment

Shugaban Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya Mista Ola Olukoyede ya ce Najeriya nada karfin daƙile matsalar cin hanci da rashawa a faɗin ƙasar, amma fa idan aka haɗa ƙarfi da ƙarfe.

 Ola Olukoyede ya yi wannan kira ne a ranar Talata 1 da watan Oktoba,  cikin saƙon  bikin ranar ƴancin kai karo na 64.

Shugaban hukumar ya ƙara da cewa hukumar ta EFCC ta himmatu wajen ganin Najeriya ta zama ƙasa da ta kawar da wannan mummunar ta’ada ta cin hanci da rashawa.

Mista Ola Olukoyede ya roki ƴan Najeriya da su bada haɗin kai ga hukumar domin ganin ta kakkaɓe cin hanci da rashawa baki ɗayan sa.

Rahotanni sun bayyana cewa cin hanci da rashawa dai na ɗaya daga cikin manyan matsalolin da suka dabaibaye Najeriya dama Afrika, ƙasar na fama da cin hanci da rashawa tun daga samun ƴancin kai, inda lamarin ke ƙaruwa a koda yaushe.

Masana na ganin babu ƙasar da zata samu cigaba mai ɗorewa da haɓɓakar tattalin arziki matsawar akwai cin hanci da rashwa.

 

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?