• Home  
  • Zan Iya Rantsuwa Da Alƙur’ani Ban Saci kuɗin Gwamnati Ba-Nasiru El’rufa’i
- Babban Labari - Labarai - Siyasa

Zan Iya Rantsuwa Da Alƙur’ani Ban Saci kuɗin Gwamnati Ba-Nasiru El’rufa’i

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasiru El-rufa’ ya bayyana cewa a shirye ya ke ya rantse da Al’ƙur’ani akan bai saci ko sisi daga asusun gwamnatin Jihar Kaduna ba. El’rufai ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin ganawarsa da ‘ƴan jarida El’rufa’i wanda shine gwamnan jihar kaduna daga  shekarar 2015 zuwa 2023 ya bayyana […]

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasiru El-rufa’ ya bayyana cewa a shirye ya ke ya rantse da Al’ƙur’ani akan bai saci ko sisi daga asusun gwamnatin Jihar Kaduna ba.

El’rufai ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin ganawarsa da ‘ƴan jarida

El’rufa’i wanda shine gwamnan jihar kaduna daga  shekarar 2015 zuwa 2023 ya bayyana cewa bai shiga gwamnati dan ya azurta kansa ba, sai dai domin ya hidimtawa al’umma.

A baya-bayan nan ne dai majalisar jihar Kaduna ta zargi El-rufa’I da karkatar da tsabar kudi har Naira Biliyan ɗari huɗu da arba’in da uku a lokacin da yake gwamnan jihar.

To sai dai El’rufa’I da muƙarraban gwamnatin sa na wancan lokacin sun musanta wannan zargi, inda suka bayyana shi amatsayin zance mara tushe balle makama.

Tsohon gwamnan ya ƙara da cewa da Zarar ya kammala karatunsa zai dawo fagen siyaysa domin cigaba da hidimtawa al’umma.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai