• Home  
  • Zafi Ya Fasa Tankin Ruwa A Malam Madori, Mutane Da Dama Sun  Jikkata
- Babban Labari - Labarai

Zafi Ya Fasa Tankin Ruwa A Malam Madori, Mutane Da Dama Sun  Jikkata

Wani tankin ruwa mai daukar dubban litoci ya fashe a kusa da layin dogo da ke Malam Madori, jihar Jigawa. 

Wani tankin ruwa mai daukar dubban litoci ya fashe a kusa da layin dogo da ke Malam Madori, jihar Jigawa. 

Lamarin ya faru ne da tsakar daren Alhamis, abin da ya yi sanadiyyar jikkatar mazauna yankin Shirinya Quarters.

Tankin da tsohon Sanata Muhammad Ubali Shitu Magama ya samar, na taka muhimmiyar rawa wajen samar da ruwa ga al’ummar yankin da maƙwabtansu.

Wani daga cikin mazauna unguwar (wanda ba a bayyana sunansa ba) ya ce a, “tankin ruwan na buƙatar gyara tun daɗewa, shi ya sa muke da kwamitin da ke kula da shi tare da tattara kuɗaɗen gyara daga mutanen da suke amfana da ruwan.”

Ya ce tuni aka aka garzaya da wadan da suka jikkata asibitin Malam Madori domin samun cikakkiyar kulawar likitoci, sai dai kawo yanzu ba a samu rahoton mutuwa ba.

Shugaban karamar hukumar Malam Madori, Salisu Sani Garungabas, ya yi alƙawarin ɗaukar matakin gaggawa domin tabbatar da cewa an gyara tankin, ya ci gaba da aiki kamar yadda aka saba.

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da  Jami’in yaɗa labarai na kananan hukumomin Malam Madori da Kaugama, Alhaji Musa Muhammad, ya fitar.

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000