• Home  
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Rantsar Da Barista Abdulkarim Maude Kwamishinan Shari’a
- Babban Labari - Labarai

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Rantsar Da Barista Abdulkarim Maude Kwamishinan Shari’a

A safiyar Juma’a, 3 ga oktoba, Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci rantsar da sabon kwamishinan shari’a na jihar, Baristra Abdulkarim Maude SAN, a rukunin gidajen Kwankwasiyya da kw kan titin zuwa Zariya.

ABBA KABIR YUSUF

A farkon makon nan ne dai aka bai wa Barista Abdulkarim Maude lambar ƙwarewa ta SAN (Senior Advocate of Nigeria) a kotun ƙoli da ke Abuja, babban birnin tarayya.

Sabon kwamishinan ya kafa tarihi a jihar Kano, kasancewar shi ne kwamishinan shari’a na farko mai riƙe lambar girmamawa ta SAN.

Da yake jawabi a wajen rantsuwar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga Barista Abdulkarim Maude ya zama mai gaskiya da rikon amana a dukkanin ayyukan da za a damƙa masa domin amfanin al’ummar Kano.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai