Home » Zamfara: Wasu ‘Yan Bindiga Sun Buƙaci Naira Miliyan 100 a Matsayin Kuɗin Fansa

Zamfara: Wasu ‘Yan Bindiga Sun Buƙaci Naira Miliyan 100 a Matsayin Kuɗin Fansa

by Anas Dansalma
0 comment

Yan bindigar da suka sace mutum 100, ciki har da kananan yara guda 80 a Jihar Zamfara, sun bukaci a ba su Naira miliyan 100 kafin su sake su.

Wata majiya daga daya daga cikin iyalan wadanda lamarin ya shafa ne ya shaida wa Aminiya hakan ranar Asabar.

Wani mazaunin kauyen Wanzamai da ke Karamar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara, wada ya ce sunansa Sani Wanzami, ya ce an kashi akalla mutum 80 a kauyensu, sai kuma wasu 20 a kauyukan da ke da makwabtaka da su.

To sai dai Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Kolo Yusuf, ta bakin Kakakin rundunar a Jihar, CSP Muhammad Shehu, ya bayar da tabbacin cewa jami’ansa tare da hadin gwiwar ragowar jami’an tsaro na kokarin ganin sun ceto mutanen lami lafiya.

SHEHU Ya ce tuni wata kakkarfar tawagar jami’an tsaron ta fara aikin sintiri da nufin ceto mutanen daga hannun maharan.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?