Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bukaci jama’ar sa su tashi da azumi gobe litinin da adduoi domin neman taimakon Allah.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi wa ‘yan jihar a Maiduguri a jiya Asabar.
Zulum ya yi alkawarin karfafa rundunonin sa kai, da inganta tattara bayanan sirri a matakin al’umma, da kuma tsarin daukar mataki cikin gaggawa da zarar an ga wani abu da ba aminta da shi ba, a wani yunkuri na dakile matsalar tsaro da ta sake kunno kai a jihar.
Ya ce, “A cikin ‘yan watannin nan, na nemii shawarwari daga abokan huldar mu na tarayya da shugabannin hukumomin tsaro daban-daban, ina mai farin cikin sanar da ku cewa hadin gwiwar da aka samu yanzu tsakanin jihar Borno da gwamnatin tarayya ya fi na kowane lokaci karfi.
“Muna aiki tukuru domin fito da dabarun karfafa tsaro, inganta musayar bayanan sirri, da kuma baiwa jami’an tsaronmu kayan aikin da suka dace don tunkarar barazanar da ke gabanmu,” in ji Zulum.