Home » Ƙungiyar Ƙwadago ta gargaɗi gwamnatin tarayya

Ƙungiyar Ƙwadago ta gargaɗi gwamnatin tarayya

by Anas Dansalma
0 comment
Ƙungiyar Ƙwadago ta gargaɗi gwamnatin tarayya

Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya da soki gwamnatin tarayya kan rage yawan kuɗin da ta ware domin biyan albashi ga ma’aikatan gwamnati zuwa Naira biliyan 100 a cikin ƙarin kasafin kudi da gwamnatin ta yi.

A cikin ƙunshin takardun farko, gwamnatin tarayya ta ayyana cewa za ta ware kusan Naira biliyan 210 ne wajen biyan albashi na watanni huɗu, sai dai bayan amincewa da kuma kwaskwarima da gwamnatin ta yi, sai ƙungiyar ta ga kuɗaɗen sun ragu zuwa Naira biliyan 100.

A yayin da yake magana kan wannan batu, mataimakin sakatare janar na ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa, Chris Onyeka, ya ce kamata ya yi gwamnatin tarayya ta ƙara kuɗin albashin ma’aikata ba ta rage ba.

Shi ma, shugaban sashen labarai na ƙungiyar ta ƙwadago, Benson Upah, ya ce, sam-sam ba a sanar da su cewa za a ɗau wannan mataki ba. Sai dai ya ce wannan abin mamaki ba ne gwamnatoci su yi hakan.

Haka ita ma taƙwarar NLC wato TUC, ta bakin mataimakin shugaban ƙungiyar ta ƙasa, Tommy Etim, ya ce bai kamata gwamnati ta riƙa wasa da albashin ma’aikata ba saboda wannan abu ne da ya shafi yarjejeniyar da aka ƙulla da ƙungiyoyin ƙwadagon kuma akwai shaidar hakan tare da kotu a ajiye.

Inda ya gargaɗi gwamnatin tarayya da cigaba da ƙoƙarin yin wasa da albashin ma’aikata domin ta san me hakan zai jawo mata.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi