Ƴan Bindiga Sun Sace Kansiloli Biyu da Limami A Rumfar Shayi A Zamfara

A daren Larabar da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari ƙauyen Tsauni da ke karamar hukumar Gusau, jihar Zamfara, inda suka yi garkuwa da kansiloli biyu da wani Limami.

Kansilolin da aka sace suna wakiltar mazabun Gidan Goga da Tsibiri na karamar hukumar Maradun. An ce lamarin ya faru ne a kusa da wani shingen binciken ‘yan sanda, bayan an idar da sallar Magariba.

Shugaban karamar hukumar Maradun, Honarabul Sanusi Gama, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa, waɗanda abin ya shafa suna zaune suna hutawa a wajen wani mai shayi ne lokacin da ‘yan bindigar suka zo suka sace su.

Gama ya ƙara da cewa, ‘yan bindigar sun fito ne da niyyar neman wani mutum da ba su same shi ba, lamarin da ya sa suka ɗauki matakin yin garkuwa da kansilolin da Limamin domin huce haushinsu.

A nasa ɓangaren, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce tuni jami’an tsaro suka bazu a yankin domin ceto waɗanda aka sace da kuma tabbatar da tsaro.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *