Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani shahararren dillalin miyagun ƙwayoyi tare da matasa biyar da ake zargi ’yan daba ne, a Unguwar Ja’oji da ke cikin birnin Kano.
Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Harun Kiyawa ne ya tabbatar da kamen a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
A cewarsa, wannan nasara ta nuna yadda rundunar ke ƙara ƙaimi wajen yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka a fadin jihar Kano.

Kiyawa ya ce, a wani samame da jami’an ’yan sanda na Ofishin ’Yan Sanda na Jaoji suka gudanar, sun kama Hafizu Ali, mai shekaru 25, mazaunin Unguwar Jaoji, wanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, tare da mutane biyar da ake zargi ’yan daba ne.
A yayin kamen, jami’an tsaro sun kwato miyagun ƙwayoyi da makamai masu hatsari daban-daban
