Abubakar Atiku Abubakar, ɗan tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya sha alwashin mara wa Shugaba Bola Tinubu baya domin tabbatar da sake zaɓensa a 2027.
Abubakar Atiku wanda aka fi sani da Abba, ya sha wannan alwashi ne bayan sauya sheƙa daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC mai mulkin ƙasar da ya yi a wannan Alhamis ɗin.
Aminiya ta ruwaito cewa, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya jagoranci karɓar Abubakar Atiku tare da wasu manyan shugabannin APC na shiyyar Arewa maso Gabas a Majalisar Tarayya.
Da yake bayyana ficewarsa daga PDP da kuma yi wa APC fatan samun nasara a zaɓe mai zuwa, Abba ya umarci dukkanin ’ya’yan ƙungiyarsa ta Haske Atiku da su koma APC su goyi bayan ajandar Shugaba Tinubu ta Sabunta Fata wato Renewed Hope.
- Lauyoyin hukumomin tsaro a Kano sun nemi Sheik Lawan Triump ya biya tarar bata musu lokaci bayan janye kara.
- Za mu gina katanga a iyakokin Najeriya- Ministan tsaro
Da yake yi wa Abba maraba zuwa jamiyyar, Mataimakin Shugaban APC na Kasa shiyyar Arewa maso Gabas, Kwamared Mustapha Salihu, ya yaba masa kan sauya sheƙar da ya bayyana cewa za ta ƙarfafa wa APC.
A nasa jawabin, Sanata Barau ya ce shawarar da Abba ya dauka ta sauya sheƙa zuwa APC na da nasaba ne da aƙidar amincewa da manufofin Tinubu, ba tare da la’akari da dangantakar mahafinsa ba da yake jam’iyyar adawa.
