Ƙasar Saudiyya Ta Tsawaita Zaman ‘Yan Sudan Da Suka Yi Umrah

Saudiyya ta yanke shawarar tsawaita bizar ƴan Sudan da suka je domin yin Umrah.

Kasar ta kaddamar da wani shiri da zai bai ƴan asalin ƙasar da kuma waɗanda ke zama a can, damar karɓar bakuncin ƴan Sudan bayan sauya bizarsu ta Umrah zuwa ta ziyara.

Matakin na zuwa ne bayan umarnin da Yarima Bin Salman ya bayar na yin haka wanda ke cikin ayyukan jin kai da suka ɗauka na tallafawa mutanen Sudan, a cewar kamfanin dillancin labaran Saudiyya.

Hukumar kula da fasfo a ƙasar (Jawazat), ta fara shirye-shiryen tsawaita bizar ƴan Sudan ɗin da suka je yin Umrah waɗanda kuma suka kasa komawa gida saboda faɗa da ake ci gaba da yi a ƙasarsu

Post masu alaƙa

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wata Mata Mai Shekaru 30 Da Katunan ATM 88

Abubuwa shida da suka sauya tun bayan zaɓen Najeriya na 2023

Kanawa mazauna Abuja sun gudanar da babban taro