Ƙungiyar Ƙwadago Ta Umarci Mambobin Ta Da Su Shiga Yajin Aiki

Kungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC ta umarci mambobin ta da gwamnati bata fa ra biya sabon albashi ba da su shiga yajin aiki. 

NLC ta ce za’a fara yajin aikin ne daga ranar 1 ga watan Disamba har sai sanda gwamnati da ɗauki matakin fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin.

NLC ta bayyana rashin biyan sabon albashin a matsayin yin karan tsaye ga doka da kuma jefa miliyoyin yan Najeriya cikin wani hali.

Majalisar Zartarwar NLC ta ƙara da cewa akwai yaudara da kuma bautar da ma’aikata, yanda wasu gwamnonin suka ƙi fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin.

Wannan umarnin na fitowa ne bayan da kungiyar ta gudanar da taron Majalisar zartaswa a ƙarshen makon nan, in da ta bayyana takaicin ta ga yadda gwamnonin ƙasar ke take doka.

Post masu alaƙa

JIGAWA: ‘Yan siyasa sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya gabanin zaben 2027

Sarkin Gumel Ahmed Muhammad Sani II ya rasu

Yan sanda sun kama mutane 79 tare da kwato kwayoyi da makamai a bikin Takutaha a Kano.