Wata kotu ta aike da shugaban wata kungiyar kwallon kafa gidan kaso a nahiyar Turai.

Wata kotu a kasar Turkiyya ta tasa keyar shugaban kungiyar kwallon kafa ta MKE Ankaragucu wato Faruk Koka zuwa gidan kaso har kusan tsawon shekaru hudu.

Wannan hukunci ya biyo bayan yadda ya zage gabjejen hannun da Allah ya bashi ya mangare wani alkalin wasa a kumatunsa sannan ya karamasa a gindin kunnensa.

Wannan duka ya sanya wannan alkalin wasa faduwa warwas a kasa inda sai dibansa a kayi shame-shame kamar ruwa ya kwanta.

Wannan shugaban kungiyar kwallon kafan maisuna Faruk Koca baiji dadin alkalancin wasan ba bayan da kumgiyarsa ta buga kunnen doki 1 – da kungiyar kwallon kafa Caykur Rizespor a kakar wasan da ta gabata inda shikuma ya fusata ya kwantar da wannan alkalin wasa.

A sanadiyyar wannan duka da aka yiwa alkalin wasan maisuna Meler hakan ta sa aka dakatar da fafata wasanni a kasar ta Turkiyya har tsawon makonni bakwai.

Amma a wannan rana ta Litinin kotu ta yankewa wancan shugaban kungiyar kwallon kafan ta MKE Ankaragucu hukuncin zama a gidan kaso.

Post masu alaƙa

Shugaban Hukumar kwallon Ƙafa ta Najeriya Ibrahim Gusau ya yi murabus

Man City ta dage kan Enzo Fernandez, Sao Paulo da West Ham na neman Vardy

Mahaifin Lionel Messi, Jorge, ya rasu yana da shekara 68