Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta MURIC ta buƙaci a tabbatar da adalci tare da biyan diyya ga iyalan masu haƙar ma’adinai 37 da suka mutu yayin da suke tsare a hannun hukumar tsaro da kare fararen hula ta Najeriya, NSCDC, a Jihar Neja.
A wata sanarwa da shugaban MURIC na jihar Kano, Malam Hassan Sani Indabawa, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta ce ta damu da yadda mutanen suka mutu bayan kama su a wani samame da aka kai kan masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.
MURIC ta ce idan zarge-zarge da ake yi wa hukumomin sun tabbata, hakan na nuna rashin ƙwarewa da rashin mutunta rayuwar ɗan’adam daga jami’an.
Ƙungiyar ta ce kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma yarjejeniyoyin kare haƙƙin bil’adama na duniya sun tanadi kare rayuwa da mutuncin mutanen da ke hannun jami’an tsaro.
Ta kuma nuna damuwa kan abin da ta kira yawaitar zarge-zargen take haƙƙin bil’adama da ake dangantawa da wasu jami’an NSCDC a sassan ƙasar.
A ƙarshe, ƙungiyar ta buƙaci a tabbatar da adalci ga mamatan tare da biyan diyya ga iyalansu.