Rundunar sojin Iran ta ce dakarun kare sararin samaniyarta sun harbo wani jirgin leƙen asiri na zamani mara matuƙi mai suna Orbiter a mashigar Hormuz.
A wata sanarwa da sashen hulɗa da jama’a na rundunar ya fitar ranar Lahadi, sojojin sun ce an harbo jirgin ne da misalin ƙarfe 6:30 na yamma agogon ƙasar.
Sanarwar ta ƙara da cewa dakarun kare sararin samaniyar Iran ne suka kai harin a yankin kudu maso gabashin ƙasar, inda suka lalata jirgin gaba ɗaya.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana ƙasar da jirgin ya fito ko kuma wanda yake gudanar da shi ba.
Mashigar Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin zirga-zirgar jiragen ruwa da jigilar man fetur a duniya.