Ƴan sandan Kano za su ƙara ƙaimi wajen amsa kiran gaggawa – CP Bakori

Kwamishinan ƴan sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya gudanar da taron tattaunawa da dakarun ƴan sanda da shugabannin Area Commands na Metro, Dala da Kano Central, domin ƙarfafa ingancin aiki, ɗa’a da kuma ƙara amincewar jama’a ga rundunar.

Taron ya gudana ne bisa umarnin Sifeto Janar na ƴan sandan Nijeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, na tabbatar da aikin ƴan sanda da ya dogara da bayanan sirri, haɗin gwiwa da al’umma da kuma mutunta haƙƙin ɗan Adam.

Kakakin rundunar ƴan sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.

CP Bakori ya yaba wa jami’an kan ƙoƙarinsu wajen yaƙi da laifuka, tare da umartarsu da su riƙa mu’amala da jama’a cikin ladabi, gaggauta amsa kiran neman taimako, ci gaba da sintiri da kuma gujewa cin hanci da duk wani nau’in rashin ɗa’a.

Ya kuma yi bayani kan gyare-gyaren da ake ci gaba da yi a rundunar domin inganta walwalar jami’ai, tare da yaba wa al’ummar Kano bisa goyon bayan da suke bai wa ƴan sanda.

Post masu alaƙa

Masu Garkuwa Da Janar Rabe Na Neman A Sako ’Yan Bindigar Da Ke Hannun Gwamnati

Gwamna Namadi ya dakatar da hadimansa huɗu

Ƴan sanda sun fara bincike kan mutuwar wanda ake zargi da sokawa matashi Wuƙa a Kano