Jagoran ’yan bindiga, Kachallah Muhammad, wanda ya yi garkuwa da Manjo-Janar Rabe Abubakar Batsari (ritaya) ya bukaci gwamnati ta sako ’yan uwansa da ke hannunta a matsayin sharadin sakin babban sojan.
A ranar Litinin dan ta’addan ya kira iyalan Janar Rabe, wanda shi ne tsohon Daraktan Yada Labarai na Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya.
Wani babban jami’in karamar hukumar Batsari da ya yi bayani a sirrance saboda dalilan tsaro ya bayyana cewa sun yi magana ta waya da Kachalla Muhammadu, kuma ya ba shi Janar Rabe sun yi magana da shi.
“Na yi magana Janar Rabe ta hannun Kachalla Muhammad kuma ya tabbatar mini cewa shi da mai dakinsa suna nan lafiya,” yana mai shaida wa ’yan uwa cewa masu garkuwa da su, suna kla da su, lamarin da ya rage fargabar da al’umma ke ciki game da garkuwar.
Jami’in ya bayyana cewa a yayin tattaunawar tasu, Kachalla Muhammad ya ba cewa abin da yake bukata shi ne jami’an tsaro su suka wasu ’yan uwansu da ke tsare a hannunsu.
“Ya ce yana so a sako ’yna uwanda da ke hannun gwamnati ba tare da bata lokaci ba, kuma a shirye yake a koma teburin sasanci da shi domin samun zaman lafiya a yankin Karamar Hukumar Matazu da makwabtansu da yake da iko,” a cewar jami’in.
A ranar Asabar ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi tare a matarsa a hanyar Marabar Musawa-Kafin Soli da ke Karamar Hukumar Matazu ta Jihar Katsina.
Shaidu sun bayyana cewa maharan sun fito daga cikin daji ne suka tare hanyar, inda suka bude wa motar Janar din wuta a lokacin da yake wucewa a hanyar, wadda matafiya da dama suka kaurace mata saboda yawan hare-haren ’yan ta’adda.
Sun bayyana cewa maharan sun bude wa motar Janar Rabe, inda dole ta tsaya, suka yi awon gaba da shi da matarsa zuwa cikin jeji, suka harbi direbansa, amma suka yi watsi da shi.
Damuwar dangi
Dangi da mazauna yakin Batsari sun bayyana damuwa game da garkuwa da tsohon Janar din sojan, wanda suka bayyana a matsayin babban abin tsahin hankali a gare su, musamman la’akari da irin ayyukan alherinsa da suka amfanar da su bayan ya bar aikin soja.
Wata ’yar uwarsa mai suna Mariya Ibrahim, ta bayyana shi a matsayin karfin iyalansu, ta ce sun fada a tarkon ’yan bindiga sun yi gakruwa da shi da matarsa ne a hanyarsu ta zuwa bikin daurin aure.
Ibrahim Mamman Batsari, wani mazaunin garin, ya bayyana cewa, “Tunda har aka iya yin garkuwa da babban soja, to ina ga sauran mutane, ya kamata gwamnati ta tashi ta yi abin da ya kamata.”
Aisha Abubakar Batsari, wadda ’yar uwar Janar Rabe ce, ta bayyana shi a matsayin jigo a danginsu, inta ta bukaci a kubutar da shi cikin aminci.
Wasu mazauna garin sun bayyana cewa Janar Rabe yana taimaka wa al’ummar Batsari da ayyukan raya kasa.
Wani shugaban al’umma, Haruna Mai Maganin Kwari Batsari, ya ce ko ranar da aka yi garkuwa da shi, suna jiran isowarsa domin tattauwa wasu abubuwan da suka shafi al’ummar yankin.
Wani kwarrarren masanin tsaro, Abubakar Ibrahim, ya ce garkuwa da janar din sojan ya nuna matukar karuwa da hadarin matsalar rashin tsaro a Jihar Katsina, yana gargadin cewa kungiyoyin masu laifi suna kara samun Karfin gwiwa.
“Wannan ya bayyana raunin manyan hanyoyi da Kauyuka. Idan ba a Dauki kwakkwaran mataki cikin gaggawa ba, lamarin na iya kara tabarbarewa,” in ji shi.