Gwamna Namadi ya dakatar da hadimansa huɗu

Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa, ya dakatar da wasu hadimansa huɗu daga aiki har sai abin da hali ya yi.

Wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim, ya fitar a ranar Litinin ta ce dakatarwar ta fara aiki nan take.
Waɗanda abin ya shafa sun haɗa da Abbas Makama, Babban Mataimaki na Musamman kan Kula da Ambaliyar Ruwa; Salisu Muhammad, wanda aka fi sani da Rosy Auyo, Mataimaki na Musamman kan Harkokin Kasuwanci; Ibrahim Yunusa, Mataimaki na Musamman kan Sa-ido a Fannin Ilimin Firamare; da Umar Abdulkadir, wanda aka fi sani da Alhaji Bullet Auyo, Mataimaki na Musamman kan Harkokin Noma.

Sanarwar ba ta bayyana takamaiman dalilin dakatarwar ba, sai dai ta ce matakin ya fara aiki ne nan take.

Gwamnatin jihar ta ce dakatarwar za ta ci gaba da aiki har sai an fitar da wani sabon umarni game da lamarin.

Post masu alaƙa

Ƴan sanda sun fara bincike kan mutuwar wanda ake zargi da sokawa matashi Wuƙa a Kano

Babachir Lawal ya fita daga ADC

DSS ta kama mutane 5 da ake zargi da sace ɗaliban makarantar St. Mary’s Pipiri a jihar Neja