Ɗalibai makafi 135 sun rubuta jarrabawar JAMB a Kano

Aƙalla ɗalibai 135 masu lalurar gani ne suka rubuta Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu ta 2026 (UTME) na Hukumar JAMB a Jihar Kano.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shirin ya cika shekaru 10 da ba wa ɗalibai masu nakasa damar rubuta jarrabawar tun daga shekarar 2017.

Da yake jawabi ga ’yan jarida bayan fara jarrabawar, Koodinetan cibiyar Kano, Farfesa Muhammad Yahuza Bello, ya bayyana cewa adadin ya kai fiye da kashi 25 cikin 100 na ɗaliban da ke da buƙatu na musamman a fadin Najeriya.

Ya ce cibiyar Kano, wadda aka kafa tun 2017, tana karɓar ɗalibai daga jihohin Kano, Jigawa, Katsina, Kaduna da Zamfara.

Farfesa Bello, tsohon Shugaban Jami’ar Bayero Kano (BUK), ya ƙara da cewa JAMB ta samar da masauki kyauta, abinci da tallafin sufuri ga ɗaliban a lokacin jarrabawar.

“An maida kuɗin rajista ga waɗanda suka bayyana nakasarsu tun lokacin rajista tare da shigar da sakamakon ‘O’ level mai ɗauke da aƙalla darussa biyar da suka ci. Ɗaliban suna da damar amfani da tafteta, allo da stylos ko kuma mai fassara, domin ba za su iya amfani da tsarin CBT ba,” in ji shi.

Ya ce a cikin shekaru 10 da suka gabata, fiye da ɗalibai 5,000 masu buƙatu na musamman ne suka rubuta UTME ƙarƙashin shirin, inda kashi 34 cikin 100 daga cikinsu suka samu shiga manyan makarantu.

Farfesa Bello ya bayyana shirin a matsayin “shaida ta jajircewar Najeriya wajen tabbatar da ilimi mai haɗa kowa,” yana mai cewa JAMB ta zama abin koyi a nahiyar Afirka.

A bana dai, sama da ɗalibai 530 masu nakasa daban-daban ne za su rubuta jarrabawar UTME a cibiyoyi 11 da JAMB ta ware a faɗin ƙasa.

Post masu alaƙa

Kotun Ƙoli ta ɗage Shari’ar kujerar Sarkin Kano zuwa 2027

Babbar alkalin Kano ta rantsar da sabbin alkalan kotunan shari’a su 30

Ba za mu buɗe Hormuz ba sai Amurka ta buɗe tashar ruwanmu – Iran