Gwamnatin tarayya ta maka waɗanda ake zargi da yunkurin juyin mulki a kotu

Gwamnatin Tarayya ta shigar da tuhume-tuhume 13 a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, kan wasu jami’an tsaro da ake zargi da neman yi wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu juyin mulki.

Jami’an sojin da ake zargin sun haɗa da wani mai muƙamin Birgediya Janar mai ritaya da wani Kyaftin na sojin ruwa da wani Sufeton ɗan sanda da wasu mutun 3.

Idan ba a manta ba, a shekarar 2025, Gwamnatin Tarayya ta soke bikin da aka shirya domin murnar cikar ƙasar shekara 65 da samun ’yancin kai a ranar 1 ga Oktoba.

Bayan ’yan kwanaki, rahotanni suka bayyana cewa soke bikin na da nasaba da zargin yunƙurin juyin mulki. Sai dai Hedikwatar Tsaro ta ƙaryata wannan zargi.

Daga bisani rahotanni suka bayyana cewa kama jami’an soja 16 a farkon watan Nuwamba bisa zargin hannu a yunƙurin juyin mulki, yayin da wasu biyu suka tsere.

A watan Janairu 2026, Hedikwatar Tsaro ta tabbatar da cewa akwai shirin kifar da gwamnatin Tinubu.

Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Samaila Uba, ya ce binciken da aka gudanar bisa ƙa’idojin soja ya gano wasu jami’an da ke da hannu a shirin.

Uba ya bayyana cewa za a gurfanar da jami’an a gaban kotunan soja da suka dace.

A watan Maris, iyalan jami’an da ake tsare bisa zargin juyin mulki suka roƙi Shugaba Tinubu ya ba da damar a yi shari’ar a bainar jama’a.

A wani taron manema labarai da suka gudanar a Abuja, matan sojojin da aka tsare da sauran ’yan uwa sun nemi a ba su damar ganin waɗanda ake zargin su ne jagororin shirin.

A watan Afrilu kuma, iyalan waɗannan jami’an sojoji sun gudanar da zanga-zanga a bakin Majalisar Dokoki ta Ƙasa, inda suka nemi a gaggauta shari’ar da kuma samun damar ganin ’yan uwansu

Post masu alaƙa

An kama mutum 2 a hanyar kai wa ’yan ta’adda harsasai 314

Hukumomi a Nijar sun nemi ƴan ƙasar su yi wa jami’an tsaro uziri

Yadda magoya bayan Obi da Kwankwaso suka kafa ƙungiya don samun tikitin ADC