Home » An chanja wa Nnamdi Kanu Alkali

An chanja wa Nnamdi Kanu Alkali

An chanja wa Nnamdi Kanu Alkali

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

Babban alƙalin kotun ɗaukaka ƙara ta Najeriya, John Tsoha ya canja alƙalin da ke shari’ar jagoran ƙungiyar IPOB da ke fafutikar kafa ƙasar Biafra, Nnamdi Kanu, kamar yadda shafin intanet na tashar Channels ya ruwaito.

Lauyan Kanu, Aloy Ejimakor ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar.

A baya dai mai shari’a Binta Nyako ce take sauraron shari’ar, wadda ake zargin Kanu da cin amanar ƙasa da tayar da zaune tsaye.

A watan Satumban shekarar da ta gabata ne Kanu ya buƙaci mai shari’a Nyako ta sauka daga jagorancin sauraron shari’ar, inda ya zarge ta da rashin adalci.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?