• Home  
  • An Tsaurara Matakai A Iyayakokin Najeriya Saboda Zanga-zanga
- Babban Labari - Labarai

An Tsaurara Matakai A Iyayakokin Najeriya Saboda Zanga-zanga

Gwamnatin Najeriya ta dauki matakan tsaurara tsaro a iyakokin kasar gabanin zanga-zanga da ake shirin farawa ranar Alhamis ga watan Agusta, 2024. 

Gwamnatin Najeriya ta dauki matakan tsaurara tsaro a iyakokin kasar gabanin zanga-zanga da ake shirin farawa ranar Alhamis ga watan Agusta, 2024. 

Shugabar Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa Kemi Nandap, ta ce an tsaurara matakan tsaro a dukkanin iyakokin Najeriya

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Kenneth Udo ne ya bayyana hakan a  wata sanarwar da ya fitar a madadin hukumar ranar Asabar. 

Kwanturola Janar Kemi Nandap, ta umarci dukkanin shugabannin shiyya-shiyya a Najeriya su yi hattara.

Nandap ta bukaci hukumar su ƙara sanya ido kan zanga-zangar da wasu ke shirin yi a Najeriya

Shugabar Hukumar ta kuma ce umarnin na da nufin tabbatar da cewa wasu ‘yan ƙasashen waje ba su shigo cikin ƙasar domin shiga zanga-zangar ba.

“Ta wannan hanyar ce za a tabbatar da cewa babu wani baƙon da zai iya fakewa da zanga-zangar don tada zaune tsaye a ƙasar nan,” in ji ta.

Domin tabbatar da cewa ba a samu wata matsala dangaen da wannan aiki ba, hukumar ta dakatar da dukkanin hutun wucin gadin jami’anta domin tabbatar da ba a samu matsala ba a lokacin zanga-zangar.

Kemi Nandap, ta tabbatar wa daukacin ’yan Najeriya shirin hukumar na kiyaye iyakokin ƙasar domin inganta tsaro.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai