Home » ‘Yan Najeriya Nada ‘Yancin Yin Zanga-Zanga-Bugaje

‘Yan Najeriya Nada ‘Yancin Yin Zanga-Zanga-Bugaje

by Mubarak Ibrahim Mandawari
0 comment

Tsohon ɗan majalisar tarayya kuma jigo a siyasar Arewa,  Dokta  Usman Bugaje ya bayyana cewa ‘yan Najeriya su fito suyi zanga zanga, domin nuna bacin ransu ga halin matsi da suke ciki.

Bugaje ya nuna takaicin sa kan yadda gwamnatin ke wadaka da kuɗi wajen gina gidaje da kuma siya wa shugaban ƙasa jirgin sama, duk da halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki.

Dokta Bugaje ya  bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da kafar DCL Hausa, ya koka da yadda aka bawa Mr Godswill Akpabio shugabancin majalisar Dattawa wanda a cewar sa yana da lam’a ta zargin cin hanci da rashawa.

Ya kuma yi tsokaci akan shirin zanga-zanga da ‘yan Najeriya ke shirin yi, inda yace ‘yan Najeriya  ‘yancin yin  hakan a dokar ƙasa.

Dokta Bugaje yayi kira ga matsan da suyi zanga-zangar cikin lumana ba tare da salwanta dukiyoyin mutane ko gwamnati ba.

” kar a saci kayan wani, kar a fasa shagon wani, ko lalata dukiyoyin mutane, ko kuma farwa gine ginen gwamnati.” a cewar Dokta Usman Bugaje.

Ya ƙara da cewa malamai kamata yayi su nusar da mutane kan abubuwan da bai kamata suyi ba yayin zanga -zangar, ba wai hanasu fita domin nemawa kansu mafita ba.

“wannan ka’idojin ya kamata malamai su nusar da mutane ba wai hana su zanga zangar ba. Kamata yayi su hanesu yin duk wani abu daya saɓa da doka ta ƙasa da kuma ta addini”.

A tambayar da aka yi masa shin idan aka yi masa tayin mukami a gwamnatin Bola Ahmad Tinubu zai karba, Dokta Bugaje yace sai dai bada shawara, domin shekarun sa sunyi nisa da ya kamata ya bawa matasa dama.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?