• Home  
  • Amfanin Kankana Ga Llafiyar Dan Adam
- Babban Labari - Labarai - Lafiya - Nishadi

Amfanin Kankana Ga Llafiyar Dan Adam

Masana kiwon lafiya a fannin ingantacen abinci wato dietians ko nutritions sun tabbatar da cewa kankana nada muhimmci ga lafiyar Mutum. Da yawan mutane kan sha kankaka domin zaƙin da Allah ya yi mata ba tare da sanin alfanun da take da shi ba ga lafiya. Kankana wata aba ce mai ɗauke da ruwa mai […]

Masana kiwon lafiya a fannin ingantacen abinci wato dietians ko nutritions sun tabbatar da cewa kankana nada muhimmci ga lafiyar Mutum.

Da yawan mutane kan sha kankaka domin zaƙin da Allah ya yi mata ba tare da sanin alfanun da take da shi ba ga lafiya.

Kankana wata aba ce mai ɗauke da ruwa mai zaƙi kuma mai amfani matuka ga jikin dan’adam.

Masana sun bayyana cewa kankana na da sinadarai da suka haɗa da: vitamin da minerals da antioxidants da kuma calories.

Kankana na da sinadarin da ke taimakawa wajen saukar da kumburi a jikin dan’adam, sannan tana ƙunshe da sinadaran vitamin A, C, B6, a cewar masana lafiya.

Sannan kankana na ƙara ruwa a jiki, kana ta na bada kariya daga cutar cancer wato sankara da kariya daga ciwon zuciya.

Kankana taimaka wa jiki wajen samar da ƙwayoyin garkuwa da ke yaƙi da cututtuka da kuma samun kuzari a jiki.

Sannan tana kara ƙarfin idanu da gyara fata da gashi.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai