• Home  
  • Gwamna Abba Ya Kirkiro Sabbin Hukumomi 4 A Kano
- Babban Labari - Labarai

Gwamna Abba Ya Kirkiro Sabbin Hukumomi 4 A Kano

Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rattaba hannu kan wasu dokoki  huɗu domin kafa sabbin hukumomi a jihar.

Gwamnatin Kano na daura auren zaurawa a yau

Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rattaba hannu kan wasu dokoki  guda huɗu domin kafa sabbin hukumomi a jihar.

Dokokin da ya sanya wa hannu za su samar da Hukumar Kare Hakkokin Jama’a ta Jihar Kano (KASPA), da Hukumar Kula da Tallace-tallace da Rubuce-rubuce ta Jihar Kano (KASIAA), da Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa da Zamani ta Jihar Kano (KASITDA), da kuma Hukumar Bunƙasa Ƙananan Kasuwanci da Matsakaita ta Jihar Kano (KASMEDA).

Mai magana da yawun gwamanan Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana muhimmancin waɗannan dokokin wajen ƙarfafa ƙirƙire-ƙirƙire, tallafa wa ƙananan kasuwanci, tsara tallace-tallace, inganta kare hakkin jama’a da samar da ayyuka.

Sanusi Bature ya kara da cewa an yi wadannan dokokin ne domin ƙarfafa tsarin gudanarwa na jihar da kuma haɓaka ci gaba mai ɗorewa.

Gwamnan ya jaddada cewa waɗannan hukumomi za su taka muhimmiyar rawa wajen samar da ayyukan yi, da kuma aiwatar da tsare-tsaren gwamnati yadda ya kamata.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai