• Home  
  • An Ɗaure Ɗan Kasuwa Wata 4 Saboda Satar Zakaru 2
- Babban Labari - Labarai

An Ɗaure Ɗan Kasuwa Wata 4 Saboda Satar Zakaru 2

Wata Kotun Majistare da ke Jos a ranar Juma’a ta yanke wa wani ɗan kasuwa mai suna Shederack Danlami mai shekaru 22 hukuncin daurin watanni hudu a gidan yari bisa samunsa da laifin satar zakaru biyu. 

Wata Kotun Majistare da ke Jos a ranar Juma’a ta yanke wa wani ɗan kasuwa mai suna Shederack Danlami mai shekaru 22 hukuncin daurin watanni hudu a gidan yari bisa samunsa da laifin satar zakaru biyu. 

Mai shari’a Shawomi Bokkos ta gurfanar da wanda ake tuhuma tare da yanke masa hukunci bayan ya amsa laifinsa.

Mai Shari’a Bokkos, a hukuncin da ta yanke, ta baiwa mai laifin zabin biyan tarar N20,000.

Tun da farko, ɗan sanda mai shigar da kara, sufeto Daniel Longwal, ya shaida wa kotun cewa, an kai karar ɗan kasuwar ofishin ‘yan sanda na Anglo-Jos a ranar 25 ga watan Maris, da wata tawagar ‘yan banga.

Longwal ya ce wanda aka yankewa hukuncin ya saci zakaru biyu kuma ya yankasu wanda farashin su ya kai Naira 20,000.

Mai gabatar da kara ya ce laifin ya saba wa tanadin sashe na 286 na dokar Penal Code na jihar Filato. (NAN)

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai