Masu zanga-zanga sun fito a biranen Najeriya domin kokawa kan halin da ƙasar ke ciki yayin da ƙasar ke bikin ranar dimkuraɗiyya a yau Alhamis.
A birnin Ibadan na jihar Osun masu zanga-zangar na ɗauke ne da allunan waɗanda suka ƙunshi saƙo daban-daban.
Daga cikin abin da masu zanga-zangar ke kokawa a kai akwai talauci da matsin rayuwa, waɗanda suke zargin manufofin gwamnati sun haifar.
Cire tallafin man fetur da sauye-sauye a ɓangaren kudi sun haifar da tashin farashin kayan masarufi da zubewar darajar kudin ƙasar, kamar yadda masana suka bayyana.
Sai dai gwamnatin ƙasar ta ce manufofin nata za su amfani a ƙasar a nan gaba.

