Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta kashe mayaƙa sama da 15 a wasu hare-haren da ta kai ta sama a maɓuyarsu da ke dajin Sambisa a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Air Commodore Ehimen Ejodame ya fitar, ta ce an kai hare-haren ne a ranar Laraba, 3 ga watan Satumba, a kan mayaƙa da kuma kwamandojin da ake alaƙantawa da wasu hare-haren da aka kai a baya-bayan nan.
Najeriya na fama da rikicin ƙungiyar Boko Haram da ISWAP a tsawon shekara 16, lamarin da ya haifar da asarar dubban rayuka da tarwatsa miliyoyin mutane, wani abu da ya haifar da matsalar jin-ƙai.
A baya-bayan nan al’umma a wasu yankunan jihar Borno sun shiga fargaba sanadiyyar dawowar hare-haren mayaƙan, inda a makon da ya gabata aka ruwaito yadda mayakan suka kashe kimanin mutum takwas.
Harin saman na sojojin Najeriya na zuwa ne bayan “bayanan sirri sun tabbatar da ayyukan mayakan a yankin,” kamar yadda mai maganar ya bayyana.
Ya kuma ƙara da cewa harin ya lalata kayan aikin mayakan Boko Haram da Iswap da dama.

