• Home  
  • Amfani Da Na’urori Zai Magance Matsalar Tsaro Kan Iyakokin Nijeriya – Muhammad Babandede, OFR,OCM
- Babban Labari - Labarai

Amfani Da Na’urori Zai Magance Matsalar Tsaro Kan Iyakokin Nijeriya – Muhammad Babandede, OFR,OCM

Tsohon shugaban hukumar shige da fice ta Najeriya, Muhammad Babandede, OFR, OCM, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi amfani da kimiyya da fasaha wajen magance matsalar tsaro akan iyakokin kasar. Muhammad Babandede ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da sashin Hausa na DW. Babandede ya bayyana cewa amfani da […]

Tsohon shugaban hukumar shige da fice ta Najeriya, Muhammad Babandede, OFR, OCM, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi amfani da kimiyya da fasaha wajen magance matsalar tsaro akan iyakokin kasar.
Muhammad Babandede ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da sashin Hausa na DW.

Babandede ya bayyana cewa amfani da sabbin hanyoyin fasaha zai taimaka wajen rage barazanar ta’addanci, safarar miyagun kwayoyi, da kuma shige da ficen da ba bisa ka’ida ba.

Ya kara da cewa bai kamata mutane kawai su dinga duba iya abinda ya shafi iyakokin Nijeriya da Nijar da kuma Benin da Kamaru ba, wajibi ne gwamnatin ta Sanya kudi domin kare iyakokin kasar.

A cewarsa jami’an shige da fice da kuma masu yaki da hana fasa kwauri ba za su iya kare iyakokin kasar ba, har sai an yi amfani da kimiya da fasaha ta hanyar Sanya na’urori da jirage masara matuka.

‘’ in ana so a kula da tsaro ba wai inda aka kafe aka ce iyaka, in ka tsaya a gun kace nance iyaka ai ba zai yi amfani idan ba a bada kimiya ta tsaro ba.

Ya kuma bayar da misalign cewa lokacin da yake kan aiki, sun bayar da shawarar a siyi jirage marasa matuka, don su dinga kai sumame, kuma yakamata ace hukumar tana Dawakai da za su dinga yin amfani da su wajen zagayawa amma har sai gwamnatin ta Sanya kudi za a magance matsalar.

Ya kara da cewa akwai na’urorin da za a yi amfani wajen yaki da cin hanci da rashawa da kuma safarar makamai da sauran aikata laifuka akan iyakokin Nijeriya.

‘’ kimiya zata hana cin hanci da rashawa’’ Muhammad Babandede’’.

A karshe ya ce rashin samar da na’urorin akan iyakokin kasar ya taka rawar haifar da matsalar tsaro.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000