• Home  
  • Tinubu ya umarci hafsoshin tsaro su koma Maiduguri
- Babban Labari

Tinubu ya umarci hafsoshin tsaro su koma Maiduguri

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bai wa hafsoshin tsaro umarnin komawa Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, domin su jagoranci ayyukan tsaro kai tsaye a yankin. Wannan mataki ya biyo bayan hare-haren bama-bamai da suka yi sanadin mutuwar mutane sama da 20 tare da jikkata fiye da 100. Rahotanni daga Maiduguri sun bayyana cewa wasu da […]

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bai wa hafsoshin tsaro umarnin komawa Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, domin su jagoranci ayyukan tsaro kai tsaye a yankin.

Wannan mataki ya biyo bayan hare-haren bama-bamai da suka yi sanadin mutuwar mutane sama da 20 tare da jikkata fiye da 100.

Rahotanni daga Maiduguri sun bayyana cewa wasu da ake zargin ‘yan ta’addan Boko Haram ne suka kai hare-haren a lokaci guda a sassa daban-daban na jihar, da misalin ƙarfe 7:25 na yammacin ranar Litinin

Wani jami’in tsaro ya ce hare-haren sun janyo firgici da tashin hankali a cikin al’umma musamman a kasuwanni da wuraren taruwar jama’a.

Shugaban ƙasa ya bayyana takaicinsa kan wannan lamari, inda ya ce gwamnatinsa tana da ƙudurin kawo ƙarshen matsalar tsaro a Arewa maso Gabas.

Tinubu ya umarci jami’an tsaro su ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000