• Home  
  • Mahaifiyar Nasir El-Rufai ta rasu
- Babban Labari

Mahaifiyar Nasir El-Rufai ta rasu

Mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai mai suna Hajiya Umma El-rufai ta rasu. Ɗan tsohon gwamnan, Bello El-Rufai ne ya sanar da rasuwar a ranar Juma’a, inda ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa, “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Ina sanar da al’umma cewa Allah ya yi wa kakata, Hajiya Umma El-Rufai […]

Mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai mai suna Hajiya Umma El-rufai ta rasu.

Ɗan tsohon gwamnan, Bello El-Rufai ne ya sanar da rasuwar a ranar Juma’a, inda ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa, “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Ina sanar da al’umma cewa Allah ya yi wa kakata, Hajiya Umma El-Rufai rasuwa,” in ji shi.

Marigayiyar ita ce mahaifiyar Malam Nasir El-Rufai. “Muna godiya ga Allah bisa rayuwar da ta yi. Muna addu’ar Allah ya jiƙanta da rahama. Muna buƙatar addu’arku a gare ta,” in ji shi.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da tsohon gwamnan ke tsare a hannun hukumar ICPC, inda ake ci gaba da gudanar da shari’a kan zarginsa da badaƙala a lokacin da yake gwamnan jihar Kaduna.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai