Wata babbar kotun tarayya da ke Lokoja a jihar Kogi ta yi watsi da hukuncin da ta yanke tun farko da ta umarci hukumar zaɓen Najeriya INEC ta yi wa jam’iyyar NDC rajista a matsayin jam’iyyar siyasa.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, mai shari’a Isah Dashen, alkalin kotun ya ce dole ne a saurari dukkan ɓangarorin da abin ya shafa kafin a yanke wani hukunci kan lamarin.
Kotun ta amince da buƙatar da jam’iyyar Peace Movement Party (PMP) ta shigar, inda ta ce ya kamata a ce jam’iyyar ta zama tana cikin ƙarar.
A cewar mai shari’a, hukuncin da aka yanke a baya ya saɓawa tsarin mulki domin an zartar da shi ba tare da jin ta bakin dukkan masu ruwa da tsaki ba.
Ya bayyana cewa irin wannan kuskuren ya soke gaba ɗaya duk wani abin da ya shafi hukuncin da aka yanke kan batun.
Don haka, kotun ta bayar da umarnin a sake fara shari’ar daga farko, inda INEC da PMP da kuma NDC za su kasance a matsayin ɓangarorin da ke cikin shari’ar.
Hukuncin dai ya mayar da tirka-tirkar da ake yi kan batun rajistar jam’iyyar ta NDC zuwa babbar kotun tarayya domin ci gaba da sauraren ƙarar, inda ake sa ran za a ji daga bakin dukkanin ɓangarorin da abin ya shafa kafin a yanke hukunci.

