• Home  
  • Rundunar yan sandan jihar Kano ta ceto fasinjoji 9 bayan musayar wuta da yan bindiga a hanyar Doguwa.
- Labarai

Rundunar yan sandan jihar Kano ta ceto fasinjoji 9 bayan musayar wuta da yan bindiga a hanyar Doguwa.

Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da ceto fasinjoji tara bayan wani hari da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kai kan wata motar fasinja a yankin dajin Falgore da ke karamar hukumar Doguwa. A cewar rundunar, lamarin ya faru ne lokacin da wata motar Toyota Hiace mai lambar BKK 6824 XA […]

Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da ceto fasinjoji tara bayan wani hari da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kai kan wata motar fasinja a yankin dajin Falgore da ke karamar hukumar Doguwa.
A cewar rundunar, lamarin ya faru ne lokacin da wata motar Toyota Hiace mai lambar BKK 6824 XA ke kan hanyarta daga Jos zuwa Kano.
Sanarwar da kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ta bayyana cewa wasu mutane dauke bindiga da sauran makamI sun tare motar, inda suka yi garkuwa da fasinjoji 13 daga cikin mutabe 20 da ke cikin motar.
Rundunar ta ce bayan samun rahoton lamarin, jami’an yan sanda tare sun gaggauta isa wurin, inda suka yi musayar wuta da maharan.
Wannan ne ya Kai ga ceto mutane tara, yayin da wani namiji guda ya tsere daga hannun masu garkuwar.
Sai dai rundunar ta ce har yanzu mutum uku na ci gaba da kasancewa a hannun maharan, ciki har da namiji Daya da mata biyu.
Yanzu haka an garzaya da wadanda aka ceto zuwa Babban Asibitin Doguwa domin duba lafiyarsu, kuma rundunar ta tabbatar lafiyarsu.
Kwamishinan yan sandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya ce rundunar ta kara tura jami’anta zuwa yankin tare da ci gaba da farautar maharan domin ceto sauran mutanen da ke hannunsu.
Rundunar ta kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai ga hukumomin tsaro kan duk wani abu da zai taimaka wajen yaki da laifuka, tana mai tabbatar da cewa bincike kan lamarin na ci gaba da gudana.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000