• Home  
  • ADC ta fitar da sunayen ’yan takarar gwamnanta a jihohi 28
- Babban Labari

ADC ta fitar da sunayen ’yan takarar gwamnanta a jihohi 28

Jam’iyyar ADC ta fitar da sunayen ’yan takararta na gwamna da mataimakin gwamna a jihohi 28 domin tunkarar zaɓen 2027. Jerin ya ƙunshi wasu fitattun ’yan siyasa, ciki har da tsohon ɗan takarar gwamnan Kaduna na PDP, Isa Ashiru, tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami. Sauran sun haɗa da tsohon ɗan takarar gwamnan Delta, Great Ogboru, […]

Jam’iyyar ADC ta fitar da sunayen ’yan takararta na gwamna da mataimakin gwamna a jihohi 28 domin tunkarar zaɓen 2027.

Jerin ya ƙunshi wasu fitattun ’yan siyasa, ciki har da tsohon ɗan takarar gwamnan Kaduna na PDP, Isa Ashiru, tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami.

Sauran sun haɗa da tsohon ɗan takarar gwamnan Delta, Great Ogboru, da tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Legas, na jam’iyyar LP, Gbadebo Rhodes-Vivour.

Jam’iyyar ta kuma tsayar da Sanata Ahmad Babba Kaita a Katsina da Sanata Halliru Dauda Jika a Bauchi.

Sakataren Yaɗa Labaran ADC na Ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya ce ’yan takarar za su wakilci jam’iyyar a ƙoƙarinta na ceto ’yan Najeriya a zaɓen 2027.

Za a fara yaƙin neman zaɓen gwamna na jam’iyyar daga ranar 9 ga watan Satumba 2026.

Ga jerin sunayen ’yan takarar ADC:

1. Abiya: Kalu Kalu Agu — Mataimaki: Alozie Ogidimma Darlington

2. Adamawa: Modibbo Hammantukur Ribadu — Mataimaki: Aguwa Kevin Iliya

3. Akwa Ibom: Akpanudoedehe John James — Mataimaki: Nsien Mkpombuk Tommy

4. Bauchi: Sanata Halliru Dauda Jika — Mataimaki: Sama’ila Mohammed Kabir

5. Binuwai: Herman Iorwase Hembe — Mataimaki: Abba John Abba

6. Borno: Babagana Buhari — Mataimaki: Mamman Dauda

7. Kuros Riba: Nkoyo Toyo — Mataimaki: Okwoche Andrew Adagbor

8. Delta: Great Ogboru — Mataimaki: Afiari Gloria

9. Ebonyi: Ukpai Mba Udeh — Mataimaki: Onwe Daniel Ede

10. Enugu: Ocho Obodoze Chukwuma — Mataimaki: Eze Arinze Christopher

11. Gombe: Bala Bello — Mataimaki: Bala Sani Isa

12. Jigawa: Sabo Mohammed Nakudu — Mataimaki: Musa Ya’u Balarabe

13. Kaduna: Isa Mohammed Ashiru — Mataimaki: Kantiok Irmiya Ishaku

14. Kano: Ibrahim Ali Amin — Mataimaki: Shehu Abdulkadir Bari

15. Katsina: Sanata Ahmad Babba Kaita — Mataimaki: Aminu Yar’adua Ahmed

16. Kebbi: Abubakar Malami — Mataimaki: Zagi Musa Mohammed

17. Kwara: Zakari Mohammed — Mataimaki: Olawuyi Julius Olayide

18. Legas: Gbadebo Rhodes-Vivour — Mataimaki: Gbadamosi Babatunde Olalere

19. Nasarawa: Nuhu Angbazo — Mataimaki: Ahmed Yusuf

20. Neja: Dr. Mohammed Kpautagi — Mataimaki: Musa Mamman

21. Ogun: Biodun Collins Ogundipe — Mataimaki: Muraina Oluwaranti Oluyemi

22. Oyo: Taofeek Adegboyega Adegoke — Mataimaki: Wahab Adeniyi

23. Filato: Birgediya Janar John Sunday Sura — Mataimaki: Pwajok-Kele Chundung Bitrus

24. Ribas: Gabriel Pidomson — Mataimaki: Okumgba David Amapakaye

25. Sakkwato: Manir Mohammad Daniya — Mataimaki: Isah Bello Ambarura

26. Taraba: Abubakar Umar Tutare — Mataimaki: Kwetishe Haruna Kwenyan

27. Yobe: Kassim G. Gaidam — Mataimaki: Kori Lawan Mohammed

28. Zamfara: Shinkafi Bilyaminu Yusuf — Mataimaki: Muhammad Abdulmuddalib Auwal

ADC ta ce ’yan takarar za su yi takara ƙarƙashin tutarta a zaɓen 2027, yayin da ta ke ƙoƙarin samar da babbar jam’iyyar adawa a Najeriya.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai