• Home  
  • An kama matashi kan zargi da safarar ’yan mata a Zamfara
- Labarai

An kama matashi kan zargi da safarar ’yan mata a Zamfara

An ceto wasu ’yan mata biyu masu shekaru 13 a hannun wani matashi mai shekaru 25 da ake zargi da safarar mutane a Jihar Zamfara. Dubun matashin ta cikka ne bayan da ya fada a hannun jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (NSCDC) a  Gusau, babban birnin jihar. Mai magana da yawun hukumar a jihar, […]

An ceto wasu ’yan mata biyu masu shekaru 13 a hannun wani matashi mai shekaru 25 da ake zargi da safarar mutane a Jihar Zamfara.

Dubun matashin ta cikka ne bayan da ya fada a hannun jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (NSCDC) a  Gusau, babban birnin jihar.

Mai magana da yawun hukumar a jihar, Umar Mohammad, ya sanar cewa an kama wanda ake zargin, Bala Abubakar, ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Zurmi ne, a unguwar Lalan da ke Gusau.

Sanarwar ta ce an gano sunayen ’yan matan da aka ceto da Amira Baje Ibrahim da kuma Haulatu Shaibu, dukansu ’yan asalin Ƙaramar Hukumar Zurmi ne.

Binciken farko ya nuna cewa ya ɗauko ’yan matan ne daga Ƙaramar Hukumar Shinkafi domin kai su wajen wasu mata biyu da aka bayyana sunayensu da Hadiza da Bara’atu, wadda aka fi sani da Yar Baba, a Suleja da ke Jihar Neja.

Kwamandan NSCDC na jihar, Sani Mustapha, ya ba da umarni a miƙa lamarin ga Hukumar Hana Safarar Mutane ta Kasa (NAPTIP) domin ci gaba da bincike tare da ɗaukar matakan da suka dace.

NSCDC ta sake jaddada aniyarta na yaƙi da ayyukan ta’addanci da sauran laifuffuka, tana mai cewa za a gudanar da cikakken bincike kan lamarin kuma za a gurfanar da duk wanda aka samu da hannu idan hujjoji sun tabbatar da hakan.

Hukumar ta kuma yi gargaɗin cewa ba za ta lamunci duk wani nau’in aikata laifi ba, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai wajen yaƙi da miyagun laifuffuka.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai