Hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta NCDC ta sanar da samun akalla mutane 5 da suka harbu da cutar corona a sassan kasar nan daga ranar 25 ga watan Fabarairu zuwa 31 ga watan Maris din da ya gabata.
Alkaluman da hukumar ta fitar a yau asabar sun nuna cewa sabbin kamuwa da cutar sun fito ne daga jihohin Lagos da Rivers wadanda kuma tuni aka killace su don dakile yaduwar cutar.
NCDC ta bayyana cewa mutum 4 suka harbu da cutar a jihar Lagos yayinda wani 1 ya harbu da ita a Rivers, lamarin da ke sanya fargabar yiwuwar dawowa da kuma YADUWAR cutar a sassan Najeriya.
Zuwa yanzu alkaluman NCDC na nuna cewa mutum dubu 266 da 665 suka harbu da cutar Covid-19 a Najeriyar tun daga lokacin da aka samu bullar cutar zuwa yanzu.
NCDC tace a cikin jumullar wadanda suka kamu da cutar covid-19 a kasar nan mutum Dubu 259 da 951 sun samu warkewa yayinda cutar ta kashe mutum dubu 3 da 155 a jihohin kasar 36 da birnin Abuja.