Ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasa, NLC ta yi kira da a gaggauta ɗaukar matakan daidaita darajar Naira.
Ƙungiyar ta yi kiran ne bayan ta lura da yadda tattalin arzikin ƙasar nan ke fuskantar haɗari daga wasu matsalolin da za su biyo baya idan aka bari darajar Naira ta ci gaba da faɗuwa, kuma aka ci gaba da canza dala a farashin da ake gani yanzu.
A ƙarshen mako shugaban ƙungiyar na ƙasa, Joe Ajaero, ya fitar da wata sanarwa a Abuja, wadda a cikinta ya gabatar da shawarwari da dama waɗanda gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta iya yin amfani da su, ta ceci darajar Naira.
Kungiyar ƙwadago ta NLC ta buƙaci gwamnati ta tsara yadda za ta kare martabar Naira ta hanyar sayen kayayyakin da ake sarrafawa a cikin gida kamar su motocin da ta ke saya wa jami’anta.
Haka kuma ƙungiyar ta yi kira ga jami’an gwamnati da su zama masu kishin ƙasa kuma su daina sayo kayayyakin ƙasashen waje.