A Watan Satumba Zamu Amince Da Kafa Kasar Falasdinawa: Burtaniya

Firaministan Birtaniya Keir Starmer ya ce ƙasar za ta amince da kafa ƙasar Falasɗinawa a watan Satumba a taron Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA).

Firaiministan ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya gudanar a ranar yau Talata.

Starmer ya ce hakan zai tabbata “har sai idan Isra’ila ta ɗauki matakai na kawo karshen abin da ke faruwa a Gaza, ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, ta kuma tabbatar da cewa ba za a ƙwace Gaɓar Yamma ba, har ma da cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta tsawon lokaci da za ta haifar da mafitar ƙasashe biyu”.

Firaministan ya ƙara nanata cewa babu wani bambanci tsakanin Isra’ila da Hamas kuma buƙatar da Birtaniya take da su kan Hamas suna nan – cewa dole su saki dukkan waɗanda suke garkuwa da su, su saka hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta, su kuma amince cewa ba za su saka baki a gwamnatin Gaza ba sannan su ajiye makamai.

Starmer ya ce za su ci gaba da duba lamarin da ke faruwa a Gaza gabanin taron babban zauren MDD Da za a yi don ganin yadda ɓangarorin biyu suka ɗauki matakai na samar da zaman lafiya kafin ta ɗauki mataki na karshe.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda