BY: YASIR ADAMU
Ba wa ‘yan kasuwa damar gina matatun man fetur ko kuma farfado da na gwamnati shi ne mafita ga irin kwan-gaba-kwan-baya da ake samu game da farashin man fetur Nijeriya.
Shugaban kungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu shiyyar Arewa, Alhaji Musa Yahaya Mai Kifi, ne ya bayyana haka yayin wata hira ta musamman da MUHASA game da yanayin farashin man fetur a Nijeriya.
Wannan na zuwa ne bayan wasu rahotanni dake cewa akwai yiwuwar samun karin farashin man fetur a Nijeriya wanda hakan ya sa Muhasa ya yi kokarin tabbatar da gaskiyar labarin.
A tattunawar da wakilinmu, Yasir Adamu ya yi da shugaban Kungiyar Dillalan Manfetur Shiyar Arewa, Alhaji Musa Yahaya Maikifi, ya bayyana cewa za a iya samun karin farashin idan gwamnati ta cire tallafin baki daya.
Ya kuma yi ƙarin haske game da abinda ake nufi da tallafin man fetur, inda yace rashin sanin hakikanin tallafin ne ma ya sa gwamnatin Tinubu ta cire shi.
Da yake bayani game da mafita game da wannan al’amari, ya ce dole sai gwamnati ta farfardo da matatun man fetur ɗinta ko kuma ta bai wa yan kasuwa damar samar da nasu, domin kuwa abin kunya ne a ce kasa kamar Najeriya ace tana fitar da danyen mai don tacewa.
A kwanakin baya ne dai rahotanni ɓulla da ke nuni da cewa gwamnatin tarayya na cigaba da biyan kudin tallafin man fetur, inda a cikin watan Agustan da ya gabata kawai ta kashe kimanin Naira miliyan dubu dari da sittin da tara a matsayin taimakon rage wa jama’a radadin rayuwa, amma masana na ganin cewa tallafin man fetur ne ya dawo a fakaice.
SAURARI CIKAKKEN HIRAR DA AKA YI DA ALH. MUSA YAHAYA MAI KIFI