Gwamnan Bauchi Ya Kara Nada Wa Kansa Mataimaka168

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulqadir Mohammed ya sanar da nadin karin wasu mataimaka na siyasa guda 168 da za su taimaka masa wajen tafiyar da jihar.

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado ya fitar, Gwamna Bala Mohammed ya bayyana sabbin nade-naden mutane 168 da suka hada da manyan mataimaka na musamman, mataimaka na musamman.

Wadanda aka nada sun hada da manyan mataimaka na musamman guda biyar akan harkokin siyasa da al’umma, daya akan al’amuran fansho, mataimaka na musamman 60 da sauransu.

Gidado ya jaddada cewa an kafin a nadin, an dubi cancanta, ƙwarewa da gogewa, da kuma iya shugabancin waɗanda aka nada, domin da yawa daga cikinsu tsoffin jami’an siyasa ne.

Ya bayyana matakin an gwamnan jihar Bauchi a matsayin wani bangare na dabarun karfafa harkokin mulki, kara kawo hadin kai, da kuma karfafa hanyoyin samun nasarorin gwamnatin a ajihar.

Post masu alaƙa

Gwamnatin Jigawa ta kashe kusan naira biliyan bakwai (7) domin tallafa wa ma’aikata ta fuskar noma

Jami’an tsaro sun ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Kogi

Hukumomin tsaro sun kama wanda ya kirkiri hukumar bogi a Nijeriya